2023: Bai Dace ‘Yan Najeriya su Kalla Tikitin Musulmi da Musulmi da Wata Manufa ba – Kukah
Rabaren Matthew Hassan Kukah na Sokoto yace bai dace ‘yan Najeriya su kalla tikitin Musulmi da Musulmi da wata manufa ba.
Limamin addinin Kiristan yace Najeriya bata bukatar mai ceto a 2023, shugaba nagari kuma nagartacce ake bukata yanzu.
Ya sanar da cewa ba zai yuwu a duba kabila ko addini ba a sake sagalar da makomar ‘yan Najeriya wurin wanda ba zai iya jagoranci nagari ba.
FCT, Abuja – Bishop na Catholic Diocese ta Sokoto, Matthew Kukah, a ranar Litinin, yace Najeriya bata bukatar mai ceto a 2023, amma shugaba nagari wanda zai saita kasar ba tare da duba da kabila, harshe ko addini ba.
Kukah yace ‘yan Najeriya ba za su so sake tafka wani kuskuren ba wanda ya sagalar da dukkan burinsu kan wanda suka tsammanin zai ceto su, Arise TV suka rahoto.
Limamin addinin Kiristan ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi kan gangamin zaben 2023 dake gabatowa wanda National Institute for Legislative and Democratic Studies (NILDS) da Kukah Centre suka shirya.
Shugaban majalisar dattawam Najeriya, Ahmed Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila duk sun halarci wurin.
Limamin kiristan yace ba a sarrafa tsarin siyasar kasar nan ba yadda ya dace na tsawon lokaci. Yace bai dace kurar da tikitin Musulmi da Musulmi ta tada a kasar nan na jam’iyyar APC ta tashi ba.
Read Also:
Lawan ya nuna damuwa game da yadda ake yakin neman zabe da kuma yadda ake karkatar da yakin neman zabe zuwa nau’i na cin zarafi na jam’iyyun da ke takara kujerun siyasa a 2023.
Gbajabiamila ya bayyana matsayar Lawan kan bukatar jam’iyyun siyasa, da ‘yan takararsu, da masu magana da yawunsu kan su mayar da hankali.
Shugaban majalisar ya yi gargadin cewa tuni wasu mutane ke karya dokar gudanar da zabe a lokacin zabe. Ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta kula da irin wadannan abubuwan da ke faruwa.
Da yake gabatar da jawabi, Kukah ya ce:
“Yan Najeriya ba sa bukatar Almasihu a wannan karon. Ba za mu iya yin kuskure ɗaya a wannan lokacin ba. Mu ne ’ya’ya, ƙarni na ƙarshe; mu ne suka bari.”
Ya bayyana cewa, a cikin yanayin da ya dace, bai kamata al’amuran addini su mamaye maganar siyasa ana dab da babban zabe ba. Ya ce akwai bukatar a bai wa ‘yan Najeriya damar tunanida kansu, ba tare da duba da kabila, siyasa ko addininsu ba.
Kukah ya ce”
“Na ji tattaunawa kan ingancin kamfen da yadda ya kamata a gudanar da wannan kamfen. Mai kamfen yana neman janyoo hankalin ku kuma babu wani laifi a cikin hakan. Ba wai ’yan siyasa ba ne mutanen banza ba; wannan ba haka nake nufi ba.
“Babban kalubale a gare mu shi ne cewa ba a gudanar da siyasar mu ta ainihi ba yadda ya dace. Babban abu mai muhimmanci a cikin siyasa shi ne bambancin.
“Kun ji ni a shekaru bakwai da suka gabata ko makamancin haka.Ban huta ba. Na sakankance cewa da mun habaka dabarunmu ta hanyar kula da banbance-banbancenmu yadda ya dace, da mun ga da kyau, wannan ne ke faruwa a sauran sassan duniya.” – Bishop yace.