Sanata Urji Kalu ya Magantu Kan Batun Tsige Shugaba Buhari

 

Sanata Orji Uzor Kalu ya magantu a kan batun tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da majalisar dattawa ta dawo zama a yau Talata.

Shugaban masu tsawatarwa a majalisar ya bayyana cewa a yanzu babu sanatan da ke ra’ayin tsige shugaban kasar domin matsalar rashin tsaro ta inganta.

Tuni dai wa’adin makonni shida da majalisar ta dibawa shugaban kasar don ya magance matsalar tsaro ko a tsige shi daga kujerarsa ta cika.

Abuja – Shugaban masu tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa yan majalisar dokokin tarayya sun dawo daga rakiyar neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kalu ya jadadda cewa matsalar rashin tsaro wacce ita ce ta asassa kira ga tsige Shugaban kasar ta inganta sosai, Leadership ta rahoto.

A tuna cewa wasu sanatoci a fadin jam’iyya mai mulki da mai adawa sun ba Shugaba Buhari wa’adin makonni shida ya magance matsalar rashin tsaro ko a tsige shi daga kan kujerarsa.

Majalisar dattawan ta tafi hutunta na shekara jim kadan bayan bayar da wa’adin kuma tuni wa’adin ya cika.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yayin da majalisar dattawan ta dawo a ranar Talata, ana ta sa ran yan majalisar za su waiwayi barazanar tsigewar da aka yiwa Buhari.

Amma Sanata Kalu, wanda ya kore fargabar cewa majalisar na iya tsige Buhari daga dawowa, ya ce babu dan majalisar da zai samar da adadin sa hannun da ake bukata don tsige imma Shugaba Buhari ko shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Kalu ya kara da cewa koda an sake gabatar da irin wannan batu a zauren majalisar dattawan, zata mutu murus da kanta.

Kalu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin da dawowar majalisar dattawa bayan hutun watanni biyu.

Ya ce:

“Batun tsigewar lamari ne da babu ita. Babu wanda ke magana a kanta. Koda sun yi kokarin yi, ba za su yi nasara ba saboda muna da yawan hana hakan.

“Babu laifi dan dan majalisa ya zo da barazanar tsigewa amma shin za su yi nasara? A’a! Don haka, a iya sanina, babu wani tattaunawa game da tsige Buhari saboda tsaro ya inganta.

“Muna ta haduwa da shugabannin tsaro kuma wasu daga cikinsu sun kasance a wajen kuma za su iya tabbatar da cewa lamarin tsaro ya inganta kuma zai ci gaba da inganta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here