Binciko Abubuwan da Aka Sace: ‘Yan Najeriya Sun Koka Kan Yadda ‘Yan Sanda ke Karbar Kudade a Hannunsu

 

Damuwa ta yawaita a wurin ‘yan Najeriya a kan yadda ‘yan sanda suke warwarar kudade a hannun jama’a kafin su bi sawun wadanda aka yi garkuwa da su.

Sannan akwai rahotanni da suke bayyana yadda su ke amsar makudan kudade kamar N50,000 zuwa 100,000 don bincike a kan wayoyin ko motocin da aka sace.

Wadanda hakan ya faru da su, sun bayyana damuwar su amma rundunar ‘yan sanda ta musanta wannan batu, inda ta ce sam ba ya cikin tsarin aikin su.

‘Yan Najeriya da dama sun koka a kan yadda ayyukan ‘yan sanda suka koma ba ni gishiri in baka manda.

Hakan ya na nufin amsar makudan kudade don aiwatar da ayyukan da ya dace a ce sun yi kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

‘Yan sanda suna amsar kudade wurin bin sawun wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, barayin motoci ko kuma wayoyi da sauran su.

Bincike ya bayyana cewa, jami’an su na amsar N50,000 zuwa N100,000 daga jama’a, daidai gwargwadon kudaden da suke tunanin mutum zai iya bayarwa.

Kamar yadda wakilan Daily Trust suka rawaito, sun tattauna da ‘yan sanda masu kwarewa a fannin su inda suka bayyana cewa wannan bai dace ba kuma ba ya cikin tsarin hukumar, sun kara da bayyana cewa wannan shine “tushen rashawa a kasar nan”.

Sai dai ‘yan sandan sun musanta wannan zargin inda suka ce babu jami’in da ya kamata a ce ya amshi sisi daga hannun wani don aiwatar da aikin da ya dace a ce ya yi.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, Frank Mba, a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Daily Trust ya ce duk wanda wani dan sanda ya nemi kudi a hannun sa, ya yi gaggawar kai karar sa inda ya dace.

Daily Trust ta rawaito yadda yanzu haka babu kayan ayyukan da za a binciko ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane da suke addabar kasar nan su ka daina aiki tun wurin watanni 7 da suka gabata.

Ya kamata a ce an samar da kudin an sa a na’urar da za ta binciko wayoyin masu garkuwa da mutane bayan sun yi kira don bayyana kudin fansa ga ‘yan uwan wadanda suke sata, amma tun farkon shekarar 2021 ba a sanya ko sisi ba a na’urar.

Bincike ya kara bayyana yadda wani lokacin ‘yan sanda suke neman taimakon DSS don aiwatar da ayyukan gaggawa.

‘Yan sanda sun dade suna cece-kuce a kan rashin sakar musu kudade don aiwatar da abubuwa yadda ya dace.

Wani kwamishin ‘yan sanda wanda ya bukaci a boye sunan sa a wata tattaunawa da su ka yi a Daily Trust, ya ce N10,000 kacal ake basu duk wata, kuma shi ma ba ko wanne watan ba.

Wani dan sanda wanda ya ke aiki da jahar Legas ya ce watanni 3 kenan da ba su binciko wata wayar da aka sace ba.

A cewar sa, na’urar da suke amfani da ita wurin binciko wayoyin da aka sace ta lalace amma akwai kwararru daga China da suke aiki a kan gyara ta kuma su na sa ran za a gama kafin karshen watan Satumba.

“Ba mu iya yin komai. Yanzu haka akwai wasu kwararrun ‘yan China da suke kokarin gyara na’urar mu ta bincike.

“Baya ga wahalar da muke sha wurin binciko motocin da aka sace a arewa, babu hanyoyin sadarwa masu kyau. Kuma da su muke amfani wurin gano inda suke.

Akwai wanda ya bayyana yadda ya bayar da N50,000 wurin binciko motar sa da aka sace masa.

“Sun gano inda motar yake a Otta a jahar Ogun ana dab da sayar da ita,” a cewar sa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here