‘Yan Najeriya Suna Samun Tsaro Tare da ‘Yancin Fadin Abinda ke Ransu a Karkashin Mulkin Jonathan fiye da mulkin yanzu – J.Martins
Fitaccen mawakin nan Martin Okwun, wanda aka fi sani da J. Martins, ya roki yafiya daga wurin Goodluck Jonathan.
Ya ce tsohon shugaban kasan Najeriya ya jure caccaka da kalubale tare da zagin da jama’a suka dinga masa.
Ya ce hatta rashawa da gwamnatin Buhari ke ikirarin yaki da ita, karuwa kawai take yi fiye da zamanin Jonathan Martin Okwun, mawakin da aka fi sani da J. Martins, ya roki Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya da ya yafewa ‘yan Najeriya da suka ci amanarsa tare da kiransa da miyagun sunaye yayin mulkinsa.
Read Also:
Mawakin yana kwatanta yanayin rashin tsaro karkashin mulkin tsohon shugaban kasan da kuma na wanda ya gaje shi, Muhammadu Buhari, a wata wallafarsa ta Instagram a ranar Talata.
Jonathan ya sha mugun kaye a kokarinsa na zarcewa mulkin kasar nan wa’adi na biyu, a hannun dan takarar jam’iyyar APC.
Masu caccakarsa a wancan lokacin sun ce bai yi kokari ba wurin shawo kan matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Amma Buhari yana fuskantar makamancin lamarin a halin yanzu inda ‘yan Najeriya ke kokawa a kan yaduwar rashin tsaro da sauran kalubale da kasar nan ke fuskanta.
Kamar yadda mawakin ya sanar, ‘yan Najeriya suna samun tsaro tare da ‘yancin fadin abinda ke ransu a karkashin mulkin Jonathan fiye da mulkin yanzu.
Hakazalika, mawakin ya zargi cewa a fannin rashawa, an zargi gwamnatin Jonathan da cin rashawa amma a halin yanzu kara yawa take yi.