Bata-Gari Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda a Jahar Sokoto

Jahar Sokoto na daga cikin jahohin arewa da suka fara fuskantar babban kalubale na tsaro.

Wasu gayyar ‘yan daba a jahar arewa maso yamman sun kai hari ofishin ‘yan sandan inda suka kone shi.

‘Yan daban sun kone har da motar wani babban dan sanda tare da motocin sintiri guda biyu da aka ajiye a ofishin.

A ranar Talata, 27 ga watan Afirilun 2020, ‘yan daba a jahar Sokoto sun kone ofishin ‘yan sanda dake karamar hukumar Kware ta jahar.

Gungun ‘yan daban da suka kunshi matasa, sun isa ofishin ‘yan sandan inda suka dinga ihu tare da jaddda cewa akwai wasu wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane amma aka sake su.

‘Yan daban sun fi karfin ‘yan sandan inda suka rinjayi jami’an tsaron dake gadin ofishin kuma suka koneshi tare da motar DPO da kuma motocin sintiri guda biyu.

Ya kara da cewa matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin wandanda ake zargin kuma sun raunata wani. Rundunar ‘yan sandan jahar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta, ASP Abubakar Sanusi.

Sanusi ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa an kama wadanda ake zargin tun farko ne bayan binciken da aka yi aka gano da hannunsu a wata garkuwa da mutane da aka yi a yankin.

Lamarin ya auku ne bayan kwanaki kadan da hukumar ‘yan sandan jahar Kebbi ta tabbatar da kisan jami’anta tara a karamar hukumar Sakaba ta jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here