2015: ‘Yan Najeriya Sunyi Tsokaci Akan Kalaman Osinbajo
Sakamakon kashe-kashen da ‘yan Boko Haram suke yi a Najeriya, mutane sun yi wani waiwaye adon tafi.
‘Yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo wata wallafa da yayi a Twitter a 2015 lokacin yana kamfen.
A ranar 8 ga watan Fabrairun 2015 ne Osinbajo yace in dai Jonathan bai iya kare rayukan al’umma ba, ya cancanci a tsige shi.
Read Also:
Sakamakon kashe-kashen da ‘yan Boko Haram suke tayi a Najeriya, ‘yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan wata wallafarsa da yayi a 2015 a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Lokacin da Osinbajo yake kamfen a 2015, ya wallafa; “Idan shugaban kasa yace ba zai iya kulawa da rayuka da kuma dukiyoyin al’umma ba, tabbas laifi ne da yayi wanda ya cancanci a tsigeshi.”
Ya yi wannan wallafar ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2015, wanda mutane suka yi ta tsokaci suna yabonsa.