Mulkin ƴan Najeriya na da Wuyar Sha’ani – Buhari
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ya mulki Najeriya da iyakar iyawar da Allah ya ba shi.
Buhari ya bayyana haka ne a tattaunawa da gidan talbijin na ƙasa (NTA). Sai dai ya ce ya bar wa mutane su yi alƙalancin ko ya yi ƙoƙari ko kuma akasin haka.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce harkokin cikin gida sun dabaibaye gwamnatinsa, har ta kai ba ya damuwa da al’amuran ƙasashen waje a matsayinsa na shugaban ƙasa.
Ya ce babban ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa, shi ne batun rashin tsaro da ya addabi ƙasar.
Sai dai, ya ce bayan ƙoƙari da gwamnatinsa ta yi wajen kyautata tsaro, hakan ya janyo mutane daga ciki da wajen ƙasar zuwa don zuba jari.
Buhari ya ce bai yi ƙoƙarin azurta kanshi ba, kamar wasu hamshakan Najeriya, musamman ma ta hanyar mallakar filaye, da gidaje da kuma motoci lokacin da yake mulki.
“Dalilin haka ne ma ya sa nake rayuwata cikin kwanciyar hankali bayan na bar mulki,” in ji Buhari.
Ya ce wasu ƴan Najeriya sun yi yunƙurin kafa masa tarko ta hanyar ɓullo masa da abubuwa da yawa.
Ya ce: “Na yi ƙoƙarin kaucewa tarkon da suka ɗana min saboda na san cewa muddin suka samu nasara a kaina, to za su yi amfani da damar wajen tatse ƙasa.
‘Wasu tsiraru sun ƙwace ikon gwamnatina’
Tsohon shugaban ƙasar ya ce wasu tsiraru sun ƙwace iko da harkokin gwamnatinsa lokacin da yake mulki.
Buhari ya ce akwai tabbacin haka ta faru a tsawon mulkinsa na shekara takwas.
Idan za a iya tunawa, a 2016, uwargidan tsohon shugaban ƙasar, Aisha Buhari ta yi zargin cewa wasu tsiraru sun mamaye gwamnatin mijinta, sai dai Buhari ya ƙi gaskata hakan a lokacin.
Ya ƙara da cewa babu wanda ya taka doka kuma aka bari ya tafi ba tare da an hukunta shi ba.
‘Mulkin ƴan Najeriya na da wuyar sha’ani’
Har ila yau a tattaunawar tasa da Gidan Talbijin na Ƙasa (NTA), Buhari ya ce mulkin ƴan Najeriya na da wuyar sha’ani.
Ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa a tsawon shekara takwas da ya ɗauka yana mulkin ƙasar.
Read Also:
Ya ce akwai wuya matuƙa a ɓangaren mulkar ƴan Najeriya, saboda “suna tunanin cewa su ya kamata su karɓi ragama ba kai ba”.
“Allah ya ba ni damar mulkar ƙasata, sai dai na yi iyakar ƙoƙarina. Sauran kuma ya bar wa ƴan Najeriya su yi alƙalanci.
“Ƴan Najeriya na da wuyar sha’ani. Mutane sun san haƙƙinsu. Suna ganin su ya kamata su kai inda kake, ba kai ba.
“Don haka suna sa ido kan duk wani taku da za ka yi. Kuma sai ka tsaya da ƙafarka dare da rana domin tabbatar da cewa kana da isasshen ƙwarewa,” in ji Buhari.
Da aka yi masa tambaya kan ƙimar da yawa cikin waɗanda ke zagaye da shi lokacin mulkinsa, tsohon shugaban ƙasar ya ce “damuwarsu ce “inda ya ƙalublanci mutanen da suka caccake shi kan abin da suka yi wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Buhari ya ce ya bar mutanen da ya ɗorawa nauyi kan wani abu, su yi aikinsu yadda ya kamata, inda ya jaddada cewa ko da shi aka bai wa damar ba zai yi wani abu na daban ba karkashin tsarin da Najeriya take a yanzu.
‘Abin da ya sa na amince da sauya fasalin takardun kuɗi’
Da yake mayar da amsa a tattaunawar kan abin da ya sa ya sauya fasalin takardun kuɗi, tsohon shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, ya ce ya amince da batun ne domin gano waɗanda suka ɓoye kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya.
“Ko ƴan Najeriya sun so ko sun ki, mu ƙasa ce da ba ta ci gaba ba. Kuma a irin wannan yanayi, akwai mutanen da ba su damu ba buƙatarsu ita ce ta samun kuɗi ta kowace irin hanya.
“Hanya ɗaya tilo da zan daƙil irin waɗannan mutane shi ne nuna gaskiyata a fili ba tare da nuna shakku a kaina ba…ina ganin muna da hanya mai tsawo idan muna son kawo gyara a matsayinmu na ƙasa mai tasowa,” in ji Buhari
Ya ce ainihin abin da ya sa aka amince da sauya fasalin takardun kuɗi shi ne ƙoƙarin tabbatarwa ƴan Najeriya cewa babu hanya mai sauki idan ana son samun kyakkyawar shugabanci.
“Mutane sun yi ta min dariya saboda ba ni da kuɗi, saboda ba zan iya sayan duk wata dama da nake so ba. Haka ɗabi’un ƴan Najeriya yake,” in ji Buhari.
Buhari ya kuma ce ba ya da tabbacin cewa ya cimma dukkan abubuwan da ya tsara cimma su a matsayinsa na shugaban Najeriya daga 2015 zuwa 2023, inda ya ce “ba na kewar barin ofis”.