Rundunar ‘Yan Sanda ta Kama ‘Yan ‘One Chance’ a Jihar Nasarawa
Rundunar ƴan sandan Najeriya, reshen jihar Nasarawa sun kama wasu mutane biyu da ake zargi ƴan fashi da makami ne da ake kira ‘One Chance’ waɗanda kuma suke gudanar da harkokinsu a babbar hanyar Akwanga zuwa Keffi.
Kakakin rundunar Ramhan Nansel ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna mutanen da ake zargi suna bayyana kansu a matsayin direbobin tasi domin ɗaukan fasinjoji, sannan su kai su wani waje tare da kwashe masu kuɗinsu da kayayyakinsu, sannan kuma su yasar da fasinjojin su kuma tsere.
Read Also:
Mutanen da ake zargi sun tabbatar da aika-aikar da suke inda suka ce sun shafe fiye da shekara 10 suna yi wa mutane fashi.
Sun ƙara da cewa ko a baya-bayan nan an sako su daga gidan gyaran hali na Shendam a jihar Filato saboda aikata makamancin wannan laifin bayan da suka kammala hukuncin da aka yanke masu.
Kayan da aka gano a hannunsu akwai mota ƙirar Toyota da wata adda da guduma.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Nasarawa Umar Shehu Nadada ya bayar da umarnin a gurfanar da mutanen biyu gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya kuma bai wa jama’a tabbaci cewa rundunar za ta ci gaba da aikin kakkaɓe miyagun laifuka a jihar, yana mai neman haɗin kansu wajen cimma ƙudirin.