‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 2 da Zargin Sayar da Jabun Sababbin Kuɗi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu a kudancin Najeriya ta ce ta kama mutum biyu da zargin sayarwa tare da yin ciniki da jabun sabuwar takardar naira N1,000 ranar Juma’a.
Cikin sanarwar da fitar ranar Juma’a, rundunar ta ce ta kama Joseph Chinenye mai shekara 39 da Onyeka Kenneth Ezeja mai 29 ɗauke da tsabar kuɗin jabu naira 180,000.
Read Also:
An kama su ne yayin da suke ƙoƙarin sayar wa wani ɗan POS da kuɗin bayan sun yi amfani da su sun sayi man fetur, in ji sanarwar.
Ƙarancin sababbin takardun naira ya jefa ‘yan Najeriya cikin tasku tun daga makon da ya gabata, inda ɗaruruwan mutane ke hawa kan dogwayen layuka a wuraren cirar kuɗi na ATM.
Babban Bankin Najeriya CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabarairu a matsayin wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun N1,000, da N500, da N200. Amma za a ci gaba da sauya tsofaffi da sababbi bayan wa’adin.