Za mu Nuna Maka da Sauran Dattawa a Arewa – Bafarawa ga El-Rufai

 

 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai kan wasu kalamansa na baya-bayan nan.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce, Arewa ta fi karfin mutum daya, don haka ya kamata El-Rufai ta tauna kamalansa kafin ya furta.

El-Rufai ya tono batutuwa da yawa da suke da alaka da zargin yadda dattawan Arewa ke yiwa dan takarar shugaban kasa Tinubu zagon kasa.

Arewacin Najeriya – Martani ya biyon bayan kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da ke cewa babu sauran dattawa a Arewacin Najeriya, Punch ta ruwaito.

Martanin na fitowa ne daga bakin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiju Bafarawa, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa da sakin layin El-Rufai.

A cewar Barafarwa, ya kamata El-Rufai ya san kalaman da yake furtawa, domin irin wadannan sun yi kama da cin fuska da yin jam’i wajen kakaba rashin dattaku ga dukkan dattawa a Arewa.

Da yake zantawa da kafar labarai ta BBC Hausa, Malam Nasir El-Rufai ya tono batutuwa da ke alaka da yiwa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Tinubu zagon kasa, kuma yace daga dattawan Arewa ne.

A tattaunawar, an ji El-Rufai na cewa shima dattijo ne, domin shekarunsa 63 kuma baya tsoron wani dattijon Arewa da zai nuna masa yatsa.

Ba shekaru bane dattako, inji Bafarawa

Shi kuwa da yake martani ga kalaman El-Rufai, Bafarawa cewa ya yi ai ba shekaru bane dattako, ana samun mai kananan shekarun da ya san ya kamata.

A cewarsa, dattako na nufin tunani da sanin ya kamata irin na manyan mutane, wanda ana samunsa a yaro ko babba mai shekaru 100, rahoton BBC.

A cewar Bafarawa

“Sannan da ya ke magana cewa shekarun sa 63, kuma baya ganin da sauran dattijai a arewa, to mu muna ganin waɗannan maganganu akwai rashin dattijantaka a cikinsu.”

Za mu nuna maka da sauran dattawa a Arewa

A cewar tsohon gwamnan, El-Rufai ne wanda ba dattijo ba, domin a cewarsa hakan ya nuna karara a cikin kalamansa.

Daga karshe bafarawa ya sanar da El-Rufai cewa, Arewa ba sa’ar mutum guda bane, ta fi karfin mutum daya, domin duk wanda ya ja da ita ba zai gama lafiya ba.

Kuma yace dattawan Arewa za su koya masa hankali da sanin ya kamata, kuma za su ba duk wani irinsa kunya a zabe mai zuwa ta hanyar nuna masa akwai sauran dattawa a Arewa.

Kadan daga batutuwan da El-Rufai ya tabo sun hada da na sauya fasalin kudi da kuma wa’adin da CBN ya sanya na tattara tsoffi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here