Shugaba Buhari ya Kai Ziyara Jihar Nasarawa

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura jihar Nasarawa don halartar taron kamfen na jam’iyyar APC.

Ana kyautata zaton shugaba Buhari zai kaddamar da wasu sabbin ayyukan da gwamnatinsa ta yi a jihar.

Buhari na ci gaba da taya dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu kamfen a jihohin kasar nan.

Lafia, jihar Nasarawa – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura birnin Lafia a jihar Nasarawa domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatinsa ta yi, ciki har da cibiyar kayayyakin aikin noma ta AMEDI da ya gina.

Kamfanin dillacin labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa, cibiyar AMEDI na daga daga cikin abubuwan da Buhari ya gina kuma za a tuna dashi a fannin noma, Punch ta ruwaito.

Cibiyar za ta mayar da hankali ne wajen bajekolin kayayyakin aikin noma masu hade da fasaha; injuna da fasahar zamani.

Dalilin gina cibiyar AMEDI

Wannan aikin na cibiyar kayayyakin noma Buhari ya yi ta ne domin wadatar da kasar wajen samar da abincin da zai ciyar da kasa kana ta samar da ayyukan yi ga matasa.

AMEDI, aiki ne da ya ci biliyoyin kudade, kuma an yi shi ne don saukake harkar noma ga ‘yan Najeriya ta hanyar zamani.

Mataimakin shugaban hukunar NASENI, Farfesa Muhammad Haruna ya zanta da majalisa, inda ya bayyana cewa, cibiyar AMEDI za ta taimawa gwamnatin tarayya a kudurinta na samar da abinci da habaka kayan gida a Najeriya.

A cewar Haruna, za a kaddamar da wasu irin wadannan cibiyoyin a cikin wa’adin da ya saura wa Buhari a fadin kasar nan, FRCN ta ruwaito.

Za a kaddamar da sabuwar sakateriyar tarayya

Ana kuma sa ran Buhari zai kaddamar da sakateriyar tarayyar da ya gina birnin Lafia, kana zai kai ziyara fadar mai martaba sarkin Lafia kafin halartar taron gangamin APC a filin wasa na jihar.

NAN ta tattaro cewa, Buhari zai dawo Abuja bayan kammala taron gangamin kamfen na Tinubu a jihar ta Nasarawa.

A ziyarar Buhari ta jihar Kano a makon jiya, ta bar baya da kura, inda matasa suka yi zanga-zangan nuna adawa da tafiyar da wasu bangarori na gwamnatin shugaban kasan da ya kusa sauka.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here