‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sakai 41 a Jihar Katsina

 

Mazauna wasu kauyuka da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina suna zaman makoki sakamakon rasa yan uwansu da dama.

Hakan ne zuwa ne yayin da wasu yan ta’adda suka kashe a kalla Yansakai 41 tare da raunata 2 yayin wani artabu a dajin Yargoje.

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa Yansakai din sun bi yan ta’addan daji ne da nufin kwato shanu da suka sace.

Jihar Katsina – Wani artabu da aka yi tsakanin yan ta’adda da kungiyar tsaro ta yan sa kai da aka haramta ayyukansu ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 41 a Katsina.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar wa Channels TV hakan cikin sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Yansakai sun bi sahun yan bindigan ne bayan sun sace shanu Ya ce yan haramtaciyyar kungiyar ta Yansakai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan ta’addan da nufin karbo shanu da suka sace.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce mambobin haramtaciyar kungiyar sun bi sahun yan ta’addan sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta’addan suka musu harin kwaton bauna.

Sanarwar ta ce:

“Yan ta’addan sun harbi tare da kashe Yansakai 11 tare da raunta guda biyu. Kwamanda na Malumfashi ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru an kwaso gawarwakin tare da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kankara.”

Sanarwar ta kara da cewa:

“Tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa a halin yanzu suna atisaye da nufin gano wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su. Ana bincike.”

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan yan ta’adda da dama sun kai hari gidan wani Alhaji Muntari a Unguwar Audu gare, yankin Kandarawa a karamar hukumar Bakori inda suka sace shanu 50 da tunkiya 30.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here