Ba za a Samu Matsala da Na’urar BVAS ba – INEC

 

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta a Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ba su samu matsala da na’urar BVAS da ke tantance masu kaɗa ƙuri’a ba, a lokacin aikin gwajin na’urar da ake gudanarwa a faɗin ƙasar, ya kuma sha alwashin cewa ba za a samu matsala da na’urar ba a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe

Farfesa yakubu ya bayyana haka ne ranar Asabar a Abuja babban birnin ƙasar a lokacin da yake yabawa da yadda aikin gwajin ke tafiya a fadin ƙasar, bayan da ya halarci wasu rumfunan zaɓe da ake gudanar da gwajin na’urar.

“A duka rumfunan zaɓe biyu da muka ziyarta, ba mu samo rahoton matsala da na’urar ba, na’urorin suna aiki yadda ya kamata, kuma wannan shi ne rahoton da muke samu daga ko’ina a inda ake gudanar da gwajin a faɗin ƙasar nan”.

“Mun kuma yi wani tsari kamar yadda za mu gudanar a ranar zaɓe, akwai na’urorin da za mu ajiye na shirin ko ta-kwana, idan muka samu wata matsala za mu ɗauko su domin ci gaba da aiki”, in ji Yakubu

Shugaban hukumar ya ce daga wannan gwajin da ya gani, cikin ƙasa da daƙiƙa 30 ne na’urar ke tantance masu kaɗa kuri’a, kuma wannan shi ne rahoton da suke samu daga duk wuraren da aka gudanar da gwajin na’urar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here