An Tsinci Gawar Iyalan Basaraken Arewa da ‘Yan Bindiga Suka Sace

 

Jihar Taraba – Basaraken Mutumbiyu da ke jihar Taraba, Mai shari’a Sani Muhammad (mai murabus) ya ce an gano gawar matansa biyu da yaransa biyar, rahoton The Punch.

Sarkin ya fada wa wakilin Daily Trust a hirar wayar tarho cewa an gano gawarwarkin ne a safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairun 2023 har sun fara lalace wa.

Ya ce za a birne su a garin Mutumbiyu.

Kalamansa:

“An gano gawar iyalai na da masu garkuwa da mutane suka kashe kuma za a kawo su Mutumbiyu.”

Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace iyalan basaraken a gidansa da ke Jalingo kimanin makonni biyu.

Amma yaro dan shekara 14 cikin iyalan basaraken da aka sace ya tsere daga hannun masu garkuwar kwanaki biyu da suka wuce kuma an kai shi fada.

Dakaci karin bayani …

the nigerian news today

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com