Gwamnatocin Kaduna,Kogi da Zamfara Sun Kai Gwamnatin Tarayya ƙara Kan Sauya Fasalin Kuɗi

 

Gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙolin ƙasar, suna masu neman kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da tsarin wa’adin amfani da sabbin takardun kuɗi da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi, sakamokon matsalar ƙarancin sabbin kuɗin da suka ce ya jefa al’umominsu cikin mawuyacin hali.

Buƙatar da lauyan jihohin uku, AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN) ya gabatar wa kotun, ta nuna cewa jihohin arewacin ƙasar uku na bukatar Kotun ƙolin da ta tsayar da gwamnatin tarayya tare da hana CBN da bankunan ƙasar aiwatar da tsarin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi zuwa wa’adin 10 ga watan Fabrairu da CBN ɗin ya saka.

Masu shigar da ƙarar sun haɗar da kwamishinonin shari’a na jihohin uku, inda ministan shari’a na ƙasar Abubakar Malami (SAN) ke wakiltar gwamnatin tarayya a shari’ar.

Masu shigar da ƙarar su ce tun bayan bayyana fara amfani da sabbin takardun kuɗin, ake samun matsalar ƙaracin sabbin kuɗin a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara, kuma mutanen da suka kai tsoffin takardun kuɗin nasu bankuna, na shan matuƙar wahala kafin samun kuɗaɗen daga bankunan, a wasu lokutan ma ba sa samun kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau-da-kullum.

Sun ƙara da cewa wa’adin kwana 10 da gwamnatin tarayya ta ƙara ba zai isa ba wajen warware matsalar da ake fuskanta ta ƙarancin takardun kuɗin.

A ƙarshen mako ne dai Gwamnan Babban Bankin ya jaddada cewa CBN ɗin ba zai ƙara wa’adin da ya saka ba a wani taron manema labarai da ya gabatar a birnin Legas.

Article share

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here