Kotun Ƙolin Najeriya za ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Ahmad Lawan da Bashir Machina

 

A yau ne kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci game da rikicin takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar APC na ƙalubalantar Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa.

Jam’iyyar ta kafe cewa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne halastaccen ɗan takararta a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen.

Ya kuma ce kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce yana fatan Kotun Ƙolin za ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin ƙwararan hujjoji, kasancewar Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

nigerian tribune newspaper

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com