‘Yan Sanda Sun Sake Kama Mawallafin Sahara Reporters – Omoyela Sowore
‘Yan sandan Najeriya sun damke Omoyele Sowore a kan wata sabuwar zanga-zanga da ya fito.
An damke shi a babban birnin tarayya bayan bayyana a zanga-zangar #CrossoverWithProtest.
Tun a ranar Alhamis yayi wallafa a shafinsa na Twitter a kan gangamin a dukkan kasar nan.
‘Yan sandan Najeriya sun sake damke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a kan jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.
Sowore tare da wasu ‘yan gwagwarmaya sun shiga hannun ‘yan sandan bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, zanga-zangar da suka shirya a dukkan fadin kasar nan ana gobe sabuwar shekara.
Read Also:
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka arce ne suka tabbatarwa da Premium Times cewa an damke Sowore inda aka jefa shi daya daga cikin motocin ‘yan sanda bakwai da aka tura wurin zanga-zangar.
Duk da majiyoyin basu san inda aka yi da Sowore ba, Sahara Reporters ta ce yana ofishin ‘yan sanda na mayanka da ke Lokogoma a Abuja tare da wasu.
Hakazalika, an yi ta kokarin samun Sowore ta lambar wayarsa amma abun ya ci tura a safiyar Juma’a.
Har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san mutane nawa bane ‘yan sandan suka cafke yayin zanga-zangar ba.
Tun dai a safiyar Alhamis ne Sowore yayi kira ga ‘yan Najeriya da su fito zanga-zangar tare da daukar kyandira da fastoci inda za su nuna alhininsu a kan mulkin Buhari.
Frank Mba, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya bai daga wayarsa ba yayin da ake ta kiransa domin jin tsokacinsa.