ALLAH ya yi wa Iyan Zazzau Rasuwa – Alhaji Bashir Aminu

 

Allah ya yi wa Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau rasuwa.

Alhaji Bashir Aminu ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi.

Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 1 ga watan Janairun 2021 a gidansa da ke Legas Daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma.

A yau safiyar 1 ga watan Janairun 2021 ne kasar Zazzau ta tashi da alhini tare da tashin hankali.

Hakan ya faru ne sakamakon rasuwar Alhaji Bashir Aminu, mai sarautar Iyan Zazzau a masarautar Zazzau. Alhaji Bashir Aminu ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Alhaji Bashir Aminu shine dan takarar kujerar sarautar Zazzau daga gidan Katsinawa.

Hakazalika, shine ya samu kuri’u uku daga cikin kuri’u biyar na ‘yan majalisar nadin sarautar Zazzau suka saka.

Kamar yadda wani na hannun damansa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa da Legit.ng, ya ce Iyan Zazzau ya rasu a gidansa ne dake jihar Legas.

Allah ya ji kan shi da gafara. Ameen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here