Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano ta Kama Mutumin da yake Kaiwa ‘Yan Bindigan Zamfara Babura

An samu gagarumin nasara wajen yaki da yan bindigan da suka addabi Arewacin Najeriya.

Jami’an yan sanda sun damke mutumin da ke kaiwa yan bindigan babura.

An damke mutumin a Kano inda yake kaiwa yan bindiga babura a Zamfara Hukumar yan sandan jahar Kano ta damke wani mutumin kan zargin kaiwa yan bindiga Zamfara baburan da suke amfani da shi.

Kakakin hukumar yan sandan jahar, DSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyanawa BBC Hausa cewa an damke mutumin ne yayinda yake sayan baburan da yake shirin kaiwa jahar Zamfara.

Yayinda aka kaddamar da bincike, mutumin ya amda laifin sayarwa yan bindiga babura kimanin 100 a farashin N600,000 kan kowani guda.

“Yana sayar da babur Honda ACE 125, wacce aka fi sani da Boko Haram, wacce gwamnatin jahar Zamfara ta haramta amfani da ita.

Suna canza kwalin a nan Kano sai su kai wa yan bindiga a Zamfara inda suka hadawa,” Kiyawa yace. “Mun damkeshi da babura biyu.

Ya canza kwalayen kuma ya shirya kaisu Zamfara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here