Kashe Matafiya: Hukumar ‘Yan Sanda ba ta Son a Kama Sunan Kowa – Kwamishinan ‘Yan Sandan Jahar Plateau
Kwamishinan ‘yan sandan jahar Filato ya magantu kan wadanda suka hallaka musulmai a Jos.
Ya ce ba wannan ne karon farko ba, amma hukumar ‘yan sanda ba ta son a kama sunan kowa cikin lamarin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, hukumar na aiki tukuru wajen ganin an zakulo wadanda suka aikata laifin.
Jos, Filato – Kwamishinan ‘yan sandan Filato, Edward Egbuka, ya ce duk da cewa harin da aka kai kan matafiya a Jos ranar Asabar ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru ba, ‘yan sanda ba sa son a kama sunan kowa a lamarin.
Read Also:
Ya lura cewa wadanda suka kai farmaki kan matafiyan a Jos a ranar 14 ga watan Agusta ‘yan ta’adda ne da ‘yan daba wadanda ke son dagula yanayin tsaro a jahar don haifar da matsala da sace-sace.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Shugaban hukumomin tsaro a jahar ga Gwamna Simon Lalong.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamna Dr Makut Macham ya fitar a Jos, Punch ta ruwaito.
A cewarsa:
“Wadannan ‘yan ta’adda ne da ‘yan daba wadanda suke son dagula yanayin tsaro don haifar da matsala da sace-sace.
“Wannan ba shine karo na farko da haka ta faru ba. Ba ma son mu ambaci sunan kowa.”
A cewarsa, an ceto mutane 36 ba tare da sun ji rauni ba daga harin kuma suna cikin koshin lafiya, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da kama mutanen da suka aikata laifin.
Ya ba da tabbacin cewa hukumomin tsaro za su zakulo masu laifi da bata gari kuma a sanya su fuskantar fushin doka.