Nan Gaba Kaɗan Rotimi Amaechi Zai Koma PDP – Desmond Akawor

 

Shugaban PDP reshen jahar Ribas ya bayyana cewa nan gaba kaɗan Rotimi Amaechi zai koma PDP.

Shugaban yace Amaechi ya koma APC ne domin kayar da shugaban kasa a wancan lokacin, Jonathan.

A cewarsa tun da ya cika burinsa, to babu makawa zai koma asalin gidansa wato PDP.

Rivers – Shugaban jam’iyyar PDP reshen jahar Ribas, Desmond Akawor, ya nuna yakinin cewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, zai koma PDP, kamar yadda punch ta ruwaito.

Akawor ya faɗi hakane a wurin wani taro a ƙaramar hukumar Ikwerre yayin da yake karbar masu sauya sheka daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa PDP.

Akawor yace:

“Yan uwanmu dake shigowa PDP, bara in faɗa muku wani abu, duk waɗannan shugabannin da kuke gani mambobin PDP ne, sun je can ne suga wainar da ake toyawa amma zasu dawo.”

“Wata rana ministan sufuri, Chubuike Amaechi, ɗan mu ne, zai dawo gida jam’iyyar PDP. Inda ya koma, ya yi haka ne saboda wani dalili.”

Wane dalili ya kai Amaechi APC?

Shugaban PDP na Ribas ya kara da cewa Amaechi ya koma APC ne kawai domin yaga an kwace mulki daga hannun tsohon shugaba, Jonathan.

Akawor ya kara da cewa:

“Ya koma can ne yaga bayan shugaba Jonathan kuma burin shi ya cika don haka zai dawo gida PDP. Na faɗi haka amma ance kada na maimaita.”

“Amma yanzun nan a Ikwerre zan sake faɗa. Ɗan uwana, Abokina, babban abokin gwamnan mu Nyesom Wike, Rotimi Amaechi, kadawo gida PDP.”

Shugaban PDP ya yaba wa Wike

Tun da farko, shugaban PDP na karamar hukumar Ikwerre, ya yabawa gwamna Nyesom Wike da sauran shugabannin PDP na kasa da suka ceto jam’iyyar daga rugujewa.

A jawabinsa yace:

“Muna mika godiya ga gwamnan mu da sauran shugabannin PDP a Najeriya bisa warware matsalar da ta kusa rushe mu watannin da suka gabata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here