‘Yan Sandan Jahar Kaduna Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga a Zariya, Sun Kama 5

 

Gwarazan yan sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ɗauke da shanu maƙare da motar Bas a Kaduna.

Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yace jami’an yan sanda sun cafke wani sanannen ɗan bindiga da aka jima ana nema.

Hakanan kuma, gwarazan yan sanda sun samu nasarar daƙile harin sace mutane a garin Zariya, jahar Kaduna.

Kaduna – Rundunar yan sanda reshen jahar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun cafke masu garkuwa da mutane da safiyar Lahadi, kamar yadda Leadership ta rawaito.

Hakazalika rundunar ta sanar da cewa gwarazan jami’anta sun sheƙe mutum ɗaya daga cikin wasu tsagerun yan bindiga da suka yi nufin sace mutane a Zariya.

Kakakin rundunar reshen jahar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, ranar Litinin a Kaduna.

Jalige yace a ranar 26 ga watan Satumba, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, jami’an yan sanda sun kai ɗaukin gaggawa kan wani bayanin sirri da suka samu.

Legit.ng Hausa ta gano cewa jami’an sun samu rahoton cewa wata motar Bas maƙare da shanu da ake zargin na sata ne ta nufi wani wuri da ba’a sani ba a kan hanyar Barde–Keffi.

Yan sanda sun cafke sanannen ɗan bindiga

Jalige yace:

“Bisa wanna bayanan da muka samu, jami’an yan sanda na caji ofis ɗin Kafanchan sun kai ɗauki kuma suka samu nasarar kame motar, sun kama mutum 5.”

“Daga cikin waɗanda aka cafke harda wani sanannen ɗan garkuwa da mutane, wanda hukumar yan sanda ke nema ruwa a jallo, an kwato shanu 13 a hannunsa.”

Kakakin yan sandan yace waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, yayin da aka gano shanun mallakin wani mutumi ne a ƙauyen Uddah, kuma an bashi dabbobinsa.

Meyafaru a Zariya kuma?

A ɗaya ɓangaren kuma, Kakakin yan sandan ya bayyana cewa jami’ai sun dakile harin tawagar yan bindiga a Zariya, ranar Litinin.

“A ranar 27 ga watan Satumba, jami’an yan sanda sun samu kiran gaggawa ta caji ofis ɗin birnin Zariya, inda aka shaida musu cewa wasu mahara sun farmaki gidan wani mutu a Nagoyi Quaters.”

“Bayan samun bayanai, jami’an yan sanda tare da yan bijilanti bisa jagorancin DPO, sun kai ɗauki, inda suka fafata da maharan.”

“Yayin haka, jami’ai sun samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin yan bindigan, sauran kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

Yace an kai gawar wanda aka kashe ɗakin aje gawarwaki na asibitin koyarwar jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here