‘Yan Sandan Jahar Kaduna Sun Kama Mutane 2 Masu ba wa ‘Yan Bindiga Magunguna
Jami’an tsaro sun kama wasu mutum biyu da ke yi wa yan bindiga magani.
Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna ya sanar da hakan.
Ya kuma ce yan bindiga sun halaka mutane biyu a wurare biyu a jahar na Kaduna.
Gwamnatin jahar Kaduna ta ce yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargin suna yi wa yan bindiga magunguna a Buruku a karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna.
Gwamnatin ta ce a kalla mutane uku ne yan bindiga suka kashe a wurare daban daban a cikin awanni 48, Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan tsaro a harkokin cikin gida na jahar, Mr Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a Kaduna.
Read Also:
A cewarsa, a daya daga cikin harin, yan bindigan sun kai hari kauyen Rafin Roro a karamar hukumar Kajuru inda suka kashe mutum daya. Ya ce an gano harsashi 11 na AK-47 kuma jami’an tsaro na cigaba da bincike.
“Kazalika, yan bindigan sun kashe wani mutum daya a wani gari kusa da Maraban Jos a karamar hukumar Igabi.
“Yan bindigan sun kuma kashe wani mutum daya a wajen kauyen Garu, karamar hukumar Igabi, bayan sace shanu mallakar wasu mutane biyu.”
Kwamishinan ya ce jami’an tsaro sun fafata da yan bindigan, kuma sun gano daya yana yawa a daji yayin da saura suka tsere da raunin harsashi.
Ya ce gwamnan jahar Nasir El-Rufai ya nuna bacin ransa a yayin da ya yi addu’a Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma yi wa iyalansu ta’aziyya.
“Gwamnan ya jinjinawa yan sandan na jahar Kaduna bisa kamen a karamar hukumar Chikun ya kuma bukaci su cigaba da bincike kan lamarin.”