Shugaba Buhari ya Nuna Damuwarsa Kan Yawaitar Hatsarin Tankar Mai

 

Shugaban ya jajantawa al’umma da gwamnatin jahar Benue bisa hatsarin tankar mai da ya faru jiya Lahadi.

Ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya sahafa da su gaggauta daukar mataki nan ba da dadewa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yawaitar fashewar tankunan mai, yana mai tuhumar hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan gaggawa don magance lamarin, The Nation ta ruwaito.

Martanin shugaban kasar ya biyo bayan fashewar tankar da ta faru a garin Oshigbudu, yankin karamar hukumar Agatu na jahar Benue a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 12.

A wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, Buhari ya umarci hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa da kuma Ma’aikatar Sufuri, da su nemi hanyar magance lamarin cikin gaggawa.

Yayin da yake jajantawa dangin wadanda abin ya shafa, Shugaban ya ce: “Na damu da yawaitar wadannan fashewar tankuna a kan hanyoyin jama’a ko wuraren zama.

“Yakamata hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa da ma’aikatun sufuri su magance wannan cikin gaggawa.”

Sanarwar ta kara yin ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jahar Benue kan wannan lamarin, lura da cewa bai kamata a taba lamuran lafiyar jama’a ba saboda wani dalili.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa gwamnati da mutanen jahar Benue kan fashewar tankar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a karamar hukumar Agatu da ke jahar.

“Ganin cewa bai kamata a gurbata lafiyar jama’a a kowane irin yanayi ba, Shugaban kasa ya yi kira da a bi ka’idoji da hanyoyin kiyaye lafiya sosai; kuma ya kamata a aiwatar da wadannan ka’idoji ba tare da tsoro ko fargaba ba,” in ji sanarwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here