Rundunar ‘Yan sanda ta Karyata Kai Hari Kotun Majistare a Jihar Imo
A Najeriya, rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke kudancin kasar, ta yi watsi da rahotannin da wasu kafafofin watsa labarai a kasar ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan kotun majistire a jihar tare da banka ma ta wuta.
A sanarwar da kakakin rundunar ya fitar, ya ce wannan labari bashi da tushe bare makama, ta kuma yi mamaki da samu labarin hakan.
Read Also:
Ya bayyana cewa wutar lantarki ce ta janyo tashin gobara a kotun Majistare din, an kuma yi nasarar kashe ta ba tare da bata lokaci ba bisa agajin jami’an kashe gobara da jami’an tsaro.
An kuma killace harabar kotun da baza jami’an tsaro domin tabbtar da babu wanda ya shiga ciki, an kuma fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren.
Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da wasu mahara na daban suka kai farmaki kan wata al’umma cikin Enugu wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama.