Kano: ‘Yan Sanda Sun Kashe Mutane Biyu
Ana zaman dari dari a Kano bayan an zargi yan sanda da kashe wasu matasa biyu a unguwar Sharada.
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya afku ne a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba lokacin da yan sanda da ke yaki da yan daba suka isa unguwar.
Zuwa yanzu dai mahukunta basu yi tsokaci ko fitar da jawabi a kan lamarin ba.
An shiga halin fargaba a jihar Kano bayan kisan wasu mutane biyu da ake zargin yan sandan da ke yaki da yan daba a jihar da aikatawa.
Read Also:
Yayinda ba a fitar da kowani jawabi da ke tabbatar da hakan daga mahukunta ba, an tattaro cewa an harbe matasan ne a unguwar Sharada lokacin da sashin yaki da yan daba suka ziyarci yankin.
Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya nuna cewa yan sandan kan matsa wa matasa a yankin amma sai aka samu tirjiya a wannan rana ta Asabar wanda ya yi sanadiyar bude wuta da mutuwar mutum biyu
Matasan da aka kashe sune Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman (Mainasara) jaridar Daily Trust ta ruwaito. Rundunar yan sandan jihar Kano bata riga ta yi martani a kan lamarin ba yayinda aka tattaro cewa an birne mutanen da aka kashe a ranar Lahadi.