Jami’an ‘Yan Sanda 2 Sun Rasa Rayukansu a Harin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Ofishin ‘Yan Sanda a Jahar Imo
‘Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Izombe dake karamar hukumar Oguta a jahar Imo.
Harin wanda ya afku a safiyar ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai jami’an ‘yan sanda biyu sai kuma uku daga cikin maharan.
Mutane biyar sun mutu a safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Agusta, lokacin da wasu yan daba suka mamaye hedikwatar yan sandan Izombe dake karamar hukumar Oguta a jahar Imo, jaridar Punch ta ruwaito.
An tattaro cewa yayin da aka harbe ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki, uku daga cikin maharan ma sun rasa rayukansu.
Read Also:
Maharan wadanda suka yi shirin tayar da bam a ofishin sun yi musayar wuta da ‘yan sandan wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Michael Abattam, ya tabbatar da harin sannan ya kara da cewa mutane biyar da suka hada da ‘yan sanda biyu da ‘yan daba uku sun mutu a harin.
Abattam ya ce:
“A ranar 13 ga watan Agusta, da misalin karfe 02:45 na dare, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai da ake zargi mambobin kungiyar ta’addanci ta IPOB/ ESN, sun zo da yawan su don kai hari ofishin ‘yan sanda na Izombe amma ba su samu damar shiga ofishin ba saboda hanzarin mayar da martani da rundunar ‘yan sandan Imo suka yi.
“‘ Yan bindigar da suka ga ‘yan sanda sun yi artabu da su sun yi nasara, saboda karfin wutar da’ yan sandan suka samu. Sai suka gudu zuwa cikin daji kuma ana cikin haka ne aka kasha uku daga cikin bandan bindigar sannan aka kwato makansu.
“Yayin da sauran suka arce cikin daji da raunukan harsashi. Abin takaici, rundunar ta rasa manyan jami’anta biyu a harin.”