‘Yan Sandan Jahar Zamfara Sun Ceto Mutane 8 Daga Hannun ‘Yan Bindiga
Rundunar yan sanda a jahar Zamfara ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da yan bindiga suka sace a Bungudu.
Kakakin yan sandan jahar, ASP Muhammad Shehu, yace an samu wannan nasarar ne cikin ruwan sanyi.
Ya kuma yi kira ga mazauna jahar su cigaba da baiwa yan sanda goyon baya domin dawo da zaman lafiya a faɗin jahar.
Zamfara – Rundunar yan sanda reshen jahar Zamfara ta ceto mutum 8 da yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Bungudu, jahar Zamfara kamar yadda Punch ta rawaito.
Kakakin rundunar yan sandan jahar, ASP Muhammad Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Gusau.
A cewarsa yan bindiga sun yi awon gaba da mutanen zuwa sansanin su dake Kungurmi, amma jami’ai sun ceto su cikin ruwan sanyi.
Read Also:
Sanarwar tace:
“A kokarin da rundunar yan sandan jahar Zamfara take yi na kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da aka sace cikin ruwan sanyi.”
“Ɓarayin sun sace mutanen ne a ranar 25 ga watan Agusta a Kangon Sabuwa, karamar hukumar Bungudu.”
“Jami’an yan sanda sun tabbatar da an duba lafiyar mutanen da aka ceto, sannan suka binciko iyalansu, suka mika su garesu.”
Zamu cigaba da kokarin kubutar da mutanen da aka sace
ASP Shehu ya bayyana cewa rundunar yan sanda zata cigaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ceto mutanen dake hannun yan bindiga, kamar yadda vanguard ta rawaito.
Kakakin yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna jahar su cigaba da tallafawa jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro a kokarinsu na dawo da dawwamammen zaman lafiya a faɗin jahar ta Zamfara.