Kin Amsar Cin Hanci: Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano ta Karrama Jami’anta Biyu
Rundunar ‘yan sandan jahar kano ta karrama jami’anta biyu kan kin amsar cin hanci.
Hakan ya faru ne yayinda jami’an suke gudanar da aikinsu a hukumar kare hakkin masu siyan kaya.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan ne ya bayyana haka ranar juma’a Rundunar jahar Kano ta karrama wasu jami’anta biyu kan kin amsar miliyan daya wadda aka gabatar masu a matsayin cin hanci.
Kwamishinan yan sandan jahar, Samaila Dikko, yayi kira ga sauran jamian dasu yi koyi da wadannan jami’an biyu.
Read Also:
A wani jawabi daga mai magana da yawun bakin yan sandan jahar Kano, Abdullahi Kiyawa, ranar juma’a, yace Garba Rabo da Jamilu Buhari suna gudanar da aikinsu ne a hukumar kare hakkin masu siyan kaya a Jahar a yayin da aka gabatar masu da cin hancin, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Yace a yayin da suke kan aikinsu ne suka samu bayanin cewa akwai wasu gurbatattun kaya da suka kai darajar biliyoyin kudi wadanda aka ajiye a dakin ajiyar kaya a cikin garin Kano.
“Da jin haka sai jami’an biyu suka garzaya dakin ajiyar kayan,inda aka gabatar musu da cin hancin N1m.
Sai suka ki amsar cin hancin suka kwace gurbatattun kayan kuma suka damke wanda ake zargin,” A cewar Kiyawa Shima Manajan Darektan hukumar kare hakkin masu siyan kaya, Baffa Dan’agundi, ya yabawa jami’an akan rashin amsar cin hancin.
Dan’agundi yace hukumar ta yanke shawarar karrama jami’an da N1m saboda kyakkyawan halinsu da suka nuna. Ya kuma yi kira ga mutane da su cigaba da ba jami’ansu goyon baya su kuma rika godewa wadanda suka gudanar da aikinsu cikin aminci.