Hotunan Makahon da Yake Sana’ar Hannu

 

Wasu hotunan wani makaho sun yadu a kafar sada zumuntar Twitter.

A hotunan an hange makahon yana kera tasosin saka furanni.

Kuma yana hakan ne ba tare da taimakon kowa ba Nakasa ba annoba bace wacce zata kange mutum daga cimma burikanshi na rayuwa ko samun farin ciki a rayuwa, hakan yasa wani makaho daba’a san ko wanene ba yayi amfani da bajintar da Allah yayi mai madadin bara a kan titi.

A Wasu hotuna da wani mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter @ADawakee ya wallafa an ga makahon yana kera tasar saka furanni a kan hanya.

Yana amfani da hannayen shi wajen kere tasar da kyawawan duwatsun, makahon ya nuna bajintar shi kamar mai idanu.

Za’a iya amfani da tasosin furen wurin kawata gida.

Bashi da wani mai taimaka mai wurin kerawa kamar yadda aka gani a cikin hotunan kuma ba’a san musabbabin abinda yasa ya makance ba.

Mutumin wanda aka ga hotunan shi a Twitter an hange shi da guduma a hanunshi sannan da wata doguwar sanda wacce ya jingine kafarshi da ita.

‘Yan Najeriyaa da yawa sun jinjina ma wannan makaho akan banjintar sa na neman na kansa madadin bara akan titi yayinda wasu kuma suka mai addu’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here