‘Yan Sandan Najeriya Basu da Makami na Kwarai Don Yakan ‘Yan Bindiga – Gwamna Masari
Gwamna Masari na Katsina ya kalubalanci Sifeto Janar na yan sanda kan lamarin tsaro.
Masari yace ‘yan sandan Najeriya basu da makamai na kwarai don yakan yan bindiga.
IGP Alkali yace suna shirin daukan sabbin yan sanda 20,000.
Katsina – Gwaman jahar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi ikirari hukumar yan sanda ba tada isasshen jami’an da zasu samar da tsaro kan jaha mai adadin mutane milyan takwas.
Masari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Sifeto Janar na yan sanda, Alkali Usman Baba, a gidan gwamnatin jahar, ranar Alhamis, DailySun ta rawaito.
Masari yace babu isassun yan sandan da zasu iya bada tsaro a jahar Kastina.
A cewarsa:
Read Also:
“Jahar Katsina na da mutane kimanin milyan takwas amma yan sanda nawa muke da shi a Katsina.?”
“A nawa lissafin na adadin yan sandan dake kananan hukumominmu, ban tunanin muna da yan sanda 3,000 a jahar.”
“Misali sun kai 3,000, hakan fa na nufin kowani dan sanda daya na kare mutane 200,000. Ta yaya zai iya aiki?”
Yan sanda basu da isassun makamai, Masari
Masari ya kara da cewa jami’an yan sandan Najeriya basu da isassun makamai ko da tsofaffi ne ballantana sabbin makaman zamani.
Ya ce wannan shine abinda ake ciki a dukkan sauran hukumomin tsaron Najeriya.
Yace:
“Idan akayi maganar makamai kuma, me yan sanda ke da shi? Idan aka zo kan maganar sabbin makamai, nawa yan sanda ke da shi?”
“A nan, yan bindiga sun fara baiwa matasa N5,000 da kwayoyi don shiga aikin barandanci.”