Bayan Haɗuwa a Filin Jirgi: Kwankwaso ya Magantu Kan Haɗuwar Shi da Gwamna Ganduje

 

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Allah ne ya hada shi da Gwamna Ganduje a filin jirgi.

An ga hoton ‘yan siyasan biyu da ba su ga maciji a filin jirgi, lamarin da ya janyo maganganu daban-daban daga jama’a.

Sai dai Kwankwaso ya ce hanya ce kawai ta hada su daga Abuja, kuma bayan gaisawarsu kowa ya kama gaban shi.

Kano – Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jahar Kano, ya bada labarin yadda suka hadu da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, manyan ‘yan siyasan biyu sun hadu a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Abuja kuma sun hau jirgi daya zuwa Kano.

Su biyun sun yi aiki tare a shekaru masu yawa da suka gabata, sun kuma raba jaha tun bayan da Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso a shekarar 2015.

A yayin da Kwankwaso ya jagoranci jahar Kano, Ganduje ne mataimakinsa tsakanin 1999 zuwa 2003.

Kwankwaso ya yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin ministan tsaro.

Amma kuma bayan sake zaben Kwankwaso a shekarar 2015, ya sake daukan Ganduje a matsayin mataimakinsa.

A yayin zantawa da BBC hausa, Kwankwaso ya ce ya kwashe kusan sa’a 1 a wurin jira bayan an sanar da shi cewa Ganduje yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin.

“Na ce ba komai, Allah ne ya hada mu. Wurin kamar tasha ce, babu wanda zai ce wa wani ya zo ko kada ya zo. Ya zo, mun gaisa da juna.

“Mun hau jirgi daya kuma mun sauka a filin jirgi na Kano. Na zauna a gaba, don haka ni na fara sauka. Na gaida mutanen shi kuma na kama hanyata zuwa gida na,” Kwankwaso yace.

A lokacin da aka tambaye shi ko ya shawarci gwamnan kamar yadda ya saba kalubalantar wasu daga cikin tsare-tsarensa, Kwankwaso ya ce:

“A matsayinmu na Musulmi, ba sai muna jam’iyya daya ba za mu gaisa da juna. Shiyasa muka gaisa kuma na zauna a mazauni na, shi ma haka.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here