Shin Akwai Wata Yarjejeniya Tsakanin Atiku da Obi ?
Akwai jita-jitar ‘dan takaran jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sa labule da Peter Obi kwanan nan a kasar ketare.
Kwamitin yakin zaben Obi/Datti ya fitar da jawabi na musamman, yace Obi bai yi wani zaman yarjejeniya da su Atiku ba.
Masu magana da sunan jirgin yakin takarar LP a 2023 sun ce ana yada wadannan labarai ne domin tallata wasu ‘yan takara
Abuja – Ofishin yada labaran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Obi-Datti 2023, sun ce babu wata magana da aka ajiye da Atiku Abubakar.
A ranar Lahadi, Vanguard ta rahoto cewa kwamitin neman zaben takaran Obi-Datti 2023 ya fitar da jawabi game da rade-radin marawa PDP baya a zabe.
A jawabin da aka fitar a Abuja, wannan kwamiti yace makaryata ke yada wannan labari da nufin iyayen gidansu su yi kasuwa a takarar shugabancin kasa.
Read Also:
Wannan kwamitin yakin neman zabe yace ana kakaba hotunan Obi da sauran ‘yan takara saboda a rabi farin jininsa, amma a gaskiya babu batun hada-kai.
Labarin bogi ne – Obi/Datti
“A maimakon su dage wajen tallata ‘yan takaransu, wadannan miyagun mutane sun koma amfani da ‘dan takararmu domin samu suna a siyasa.
“Mun fahimci masu wannan sun gagara tallata ‘dan takararsu ne domin bai da abin da ake nema.”
“Mun san niyyar wadannan mutane na tallata labarin bogi da cewa ‘dan takaran LP, Peter Obi, ya hadu da takwaransa na PDP, sun shiga yarjejeniya.
“Wannan ba gaskiya ba ne ko ta kusa, ko ta nesa. Wuraren da Obi ya je a kasar waje, da wadanda ya hadu da su, duk ba boyayyun abubuwa ba ne.
“Amma masu yada karyayyaki sun fi sha’awar su kirkiri karya da nufin tallata ‘dan takaransu.”
Jirgin ceto al’umma
Daily Post tace jawabin ya kara da cewa Peter Obi da Datti Baba Ahmed su na takara ne domin ceto Najeriya, kuma babu abin da zai kauda tunaninsu.
Idan har Obi ya shiga zabe ne da nufin kawo canji, to ba zai hada kai da tsofaffin ‘yan siyasa ba. Jawabin yana nuni ga ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.