‘Yar Asalin Jihar Sokoto  ta fi Kowa Maki a Sakamakon Jarrabawar Shiga Karamin Ajin Sakandare

 

Dalibai a kalla 15 sun ci maki 01 kacal a jarrabawar shiga aji na farko na karamar sakandare da hukumar NECO ta shirya a shekarar 2022.

Ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayyana kididigan sakamakon jarrabawar ta 2022.

Wata dalibai yar asalin Jihar Sokoto mai suna Ajidagba Akanke ce ta fi kowa maki inda ta samu maki 201 mai biye mata kuma yar Jihar Akwa Ibom da maki 200.

FCT, Abuja – A kalla dalibai 15 ne suka ci maki 01 kacal a yayin da hukumar shirya jarrabawa da Najeriya, NECO, ta fitar da sakamakon jarrabawar shiga karamar ajin sakandare.

The Punch ta rahoto cewa jarrabawar ta NCEE da NECO ta yi na shiga ajin farko ne a kananan ajijuwan sakandare a makarantun sakandare na tarayya.

Jarrabawar ta 2022 an yi ta ne a ranar 7 ga watan Mayun 2022 a Nigeria da Jamhuriyar Benin da Togo.

Yayin bada kididdigan a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a ranar Litinin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce:

“Jihar Anambra ta zo ta uku da dalibai 5,335; cikin 5,070 sun rubuta jarrabawar yayin da 265 ba su rubuta ba. Jihar Zamfara ce ta hudu da dalibai 4,500, cikinsu 3,745 sun rubuta jarrabawar yayin da 755 ba su rubuta ba.

“Dalibar da ta fi kowa samun maki mai yawa ita ce Ajidagba Akanke, yar asalin Jihar Sokoto mai lamba 542121DG. Cibiyar da ta rubuta jarabawar ita ce Makarantar Karamar Sakandare ta Oshodi, Tolu Complex, Apapa Legas, ta kuma ci maki 201. Obot Idara, yar asalin Jihar Akwa Ibom mai lamba 550470BF ta zo na biyu da maki 200. Ta rubuta jarrabawar a Kwallejin Jiha ta Ete, Ikot Ekpene.

“Mafi mafi karanci shine 01, kuma wasu dalibai 15 daga jihohi daban-daban suka samu maki daya kacal din. Jihar da ta fi karancin daliabai da suka yi rajista ita ce Jihar Kebbi, da dalibai 74.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here