Majalisar Dattawa ta Nada Philip Tanimu Aduda a Matsayin Sabon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar

 

Majalisar dattawa ta yi sabbin nade-nade, inda ta samu sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Wannan na zuwa ne tun bayan da wanda ke kan kujerar ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai adawa.

A wasikar da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karba, an bayyana sunayen mutum biyu da aka nada.

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta nada Sanata Philip Tanimu Aduda (FCT) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Haka kuma an nada Sanata Chukwuka Utazi a matsayin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya sanar da nadin yayin da yake karanta wasiku daban-daban guda biyu dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu.

Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye ta zama babu kowa a kanta tun bayan ficewar Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu) daga PDP.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here