Kada Wanda ya Yaudare ku Cewa PDP ta Rarrabu – Gwamna Ortom
Gwamna Samuel Ortom na jahar Benue ya yi martani akan batun cewa ko zai tsaya takarar sanata bayan kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna.
 Ortom ya ce a halin yanzu dai bai yanke hukunci ba domin yana tuntubar Allah ne tukuna a kan lamarin.
 Ya ce a matsayinsa na wanda ke aiki da hukuncin Allah a kansa a koda yaushe, zai yi takara idan Ya bashi iko, sannan zai hakura idan Allah ya nemi yayi hakan.
Benue – Gwamnan jahar Benue, Samuel Ortom, ya ce har yanzu bai yanke shawara kan ko zai tsaya takarar kujerar sanata a zaben 2023 ba.
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Ortom ya fadi hakan ne a ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba yayin da yake zantawa da manema labarai.
Da yake amsa tambaya kan ko zai yi takara bayan ya kammala wa’adinsa na gwamna, Ortom ya ce zai dauki matakin ne daidai da abin da Allah ya yarda.
 “Har yanzu ina tuntubar Allah domin ba na yanke shawara ba tare da na tuntubi Allahna ba.
 Idan ya ce eh, zan ci gaba da yin takara, amma idan Ya ce a’a, zan yi biyayya da shawarar da ya yanke, ” inji shi.
Gwamnan ya kuma ce ya kamata a yi watsi da rahotannin rarrabuwar kawuna a cikin Jam’iyyar PDP, saboda mambobi suna aiki cikin hadin kai, Vanguard ta kuma rawaito.
Ya ce:
 “PDP a matsayin jam’iyya ta yi kurakurai a baya kuma ta koyi darussa da yawa daga kurakuranta kuma ta shirya tsaf don karbe shugabancin kasar daga hannun APC.
“Kada wanda ya yaudare ku cewa PDP ta rarrabu. Muna aiki tare a matsayin jam’iyya.
 “Mun hadu kuma mun amince cewa mukaman da suke arewa a yanzu su koma kudu, yayin da na kudu za su koma arewa.
 “Wannan shine ƙudirin kwamitin shiyya kuma an yarda da shi a matakin ƙasa.
“Babu wanda ya yi watsi da hukuncin. Duk yan PDP sun yarda da shi.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here