Akwai Yuwuwar Samun ƙarin Ambaliyar Ruwa – NiMet
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har yanzu halin ambaliyar ruwan da aka shiga bai kare ba.
Yankunan Arewa maso yamma, da arewa ta tsakiyane suka fi samun barazanar Ambaliyar a wannan shekarar.
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) da Hukumar Kula da Yanayin Ruwa ta ƙasa sun ja hankalin jihohin Arewa ta da na Kudu maso Gabas su yi shirin ko ta kwana.
Babban Daraktan Hukumar Farfesa Mansur Matazu ne ya sanar da hakan a Abuja ranar Talata yayin wani taro da hukumar ta shirya haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Ruwan Ruwa ta Najeriya (NIHSA) tare da tallafawa Cibiyar Kula da rayuwar Dabbobi da Ruwa ta ƙasar Birtaniya (UKCEH) bisa ga tallafin Cibiyar Kula da Ruwa ta Duniya (WMO).
Matazu, ya ce
Read Also:
“Akwai yuwuwar samun ƙarin ambaliya sakamakon samun ƙarin ruwan sama, ga kuma yadda koguna da madatsun ruwa suka cika, hakan yasa dole sai an buɗe su, kuma hakan barazana ne ga jihohin Arewa da na kudu”
“Kowace shekara, haɗuran da ke da nasaba da ruwa suna shafar miliyoyin mutane a duniya tare da rasa dukiyoyi da rayuka. Ana sa ran cewa haɗarurkan kan ƙaru a cikin shekaru masu zuwa, sabida barazanar sauyin yanayi da muke samu.
“Kun tuna, mun fitar da hasashen a cikin watan Fabrairu kuma mun bi diddigi tare da wallafa bayanai duk wata cewa ga adadin ruwa ko wani abu makamancin haka a kullum”
“Daga dukkan bayanan da muke tattarawa yanzu, ruwa yafi yawa a jihohin arewa da kuma jihohin arewa ta tsakiya, to dole za’a samu karin ruwa a madatsu game da koguna wanda zasu tumbatsa kuma su ƙara janyo ambaliyar”
Ya kara da cewa haka nan ma za’a samu ire-iren wannan ambaliyar a jihohin kudi maso yamma, baya ga jihar kogi, kamar yadda aka gani a lokoja, baya ga jihohin Kudu masu gabas wanda suma zasu fusknci kalubalen kamar yadda aka gani a jihar Anambara”.