Tinubu, Gwamnonin APC da Jiga-Jigan Jam’iyyar Sun Shiga Ganawa

 

Yanzu muke samun labarin cewa, kwamitocin jam’iyyar APC sun shiga ganawa don warware wasu matsalolin jam’iyyar.

Dan takarar shugaban kasan APC, Bola Ahmad Tinubu da gwamnonin jam’iyyar duk sun hallara domin wannan zama.

Hakazalika, akwai jiga-jigai da dama dake cikin kwamitin gangamin kamfen din APC na dan takarar shugaban kasa.

Abuja – Ganawar tawaga uku ta jam’iyyar APC da ta hada kwamitin ayyukanta na kasa (NWC) da tawagar gangamin kamfen na ‘yan takarar gwamnoni da shugaban kasa sun taru domin tattawa mai zurfi.

Ana yin wannan ganawar ne a Hilton Hotel dake babban birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ganawar, wacce aka ce ci gaban zaman tagawar ne na baya, zata kawo mafita ne da warware duk wata kimurmura a jerin mambobin majalisun kamfen na jam’iyyar a fadin kasar.

Hakazalika, zaman zai duba yiwuwar tabbatarwa tare da amincewa da jerin shugabannin PCC da gwamna Simon Lalong ya shirya.

Wadanda suka halarci taron sun hada da dan takarar shugaban kasan jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnoni da mambobin PCC na APC.

A baya an shirya yin taron ne a jiya Talata 11 ga watan Oktoba, amma aka daga saboda bikin ba da lambobin yabon kasa da gwamnatin Buhari ta yi a ranar.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here