Karin Harajin yin Waya: 1GB zai Koma N2500
Muddin aka aiwatar da wani sabon karin 5% a kan harajin yin waya, farashi za su tashi sama.
Masana suna hasashen kudin sayen data zai karu, mutane za su koma sayen 1GB a kan N2500.
Kusan kowa yana adawa da wannan shawara da Ministan tattalin arzikin kasa ta zo da shi.
Abuja – Ana tunanin farashin yin waya da ziyarar yanar gizo za su lula sosai, muddin gwamnatin tarayya ta amince da karin harajin da aka zo da shi.
Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust a ranar Litinin, 8 ga watan Agusta 2022, ya bayyana cewa karin da za a samu a Najeriya, zai iya kai kashi 100%.
Ministar kudi da tattalin arziki ta nuna gwamnati na shirin kara haraji ya kai 12.5%, wanda wannan karin zai shafi al’umma da kamfanonin sadarwa.
Wayar N20 za ta koma N40
Kwararrun masana a harkar sun nuna idan aka yi nasarar kara harajin, wayar minti guda zai iya kai N40.
A yanzu a kan yi wayar minti daya ne kan N20. Baya ga haka, idan aka kara 5%, za a rika sayen gigabyte daya na data a kan N2500, idan ba ayi wasa ba. Shakka babu, mutane za su koka a kan hakan.
Babu adalci – Sakataren ATCON
Read Also:
Sakataren kungiyar ATCON na kasa, Ajibola Olude ya soki shawarar kara haraji, yace hakan ya sabawa tsarin haraji da adalcin da gwamnati za tayi masu.
A cewar Ajibola Olude, matsalar karin kudin shi ne wasu mutane za su rasa hanyar cin abinci. A dalilin karin, ana tunani mutane da-dama za su rasa aiki.
Shugaban kungiyar NATCOMS ta masu amfani da kamfanonin sadarwa, Adeolu Ogunbanjo yace yanzu haka harajin da ake biya ta waya sun yi yawa.
Cif Adeolu Ogunbanjo yace akwai harajin VAT na 7.5% da gwamnati a ke tatsa daga katin waya, ana amincewa da sabon karin, za a bar mutane da wahala.
Ra’ayin Ministan sadarwa
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Isa Ali Pantami bai goyon bayan a kara kudin waya domin hakan zai jawo kamfanonin sadarwa su gujewa Najeriya.
Wani abin da ya fusata Ministan sadarwa da tattalin zamanin shi ne ma’aikatar kudi ba ta tuntube shi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa ba.
Wannan mataki zai jawo abin da ake sayen katin waya da aika sakonni da hawa yanar gizo ya karu. Ita gwamnati na harin samun makudan kudin shiga.
Abin ya yi yawa – ALTON
An ji labarin yadda shugaban kungiyar kamfanonin sadarwa na kasar nan watau ALTON, Gbenga Adebayo, ya nuna ba su goyon a amince da karin farashin.
Adebayo yace yanzu akwai haraji nau’i 39 da gwamnatin tarayya ta lafta masu. Idan aka kara wani kudi, kamfanonin za su bar mutanen kasar ne da wahala.