ASUU: Lauyan Najeriya ya Roki Shugabannin Bankuna da Attajirai su Shawo Kan Al’amarin

 

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) dai ta shiga yajin aikin tun a watan Fabrairu, inda ta bukaci a kara samar da kudade ga tsarin jami’o’in da kuma karin albashi ga mambobinta.

Aiwatar da yarjejeniyar da aka tattaunawa da gwamnatin Najeriya a shekarar 2009 na daga cikin abubuwan da kungiyar ta ASUU ta bukata.

Wani ma’aikacin shari’a ya roki attajiran Najeriya da su sa baki, yana mai cewa gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar magance matsalar.

Najeriya – Wani lauya, Pelumi Olajengbesi, ya roki manyan shugabannin bankuna da ’yan kasuwa attajirai da suka hada da Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdul Samad Rabiu, da Mike Adenuga da su lale Naira tiriliyan 1.1 domin biya ma ASUU bukatunsu.

Lauyan ya ce gwamnatin tarayya ta nuna halin ko in kula da kuma nuna rashin damuwa wajen warware yajin aikin ASUU da ya fara tun ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Don haka, ya bukaci ‘yan kasuwar da su tashi tsaye a yanzu kamar yadda suka yi a lokacin annobar corona, lokacin da suka ba da gudunmawar kudade ga gwamnatin Buhari.

A wata sanarwa da Legit.ng ta samo, lauyan ya ce:

“’Yan Najeriya masu kishin kasa za su iya kira ne ga manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdul Samad Rabiu, Mike Adenuga, da shugabannin bankuna da su kawo dauki ga talakawan Najeriya da ‘ya’yansu da ba sa zuwa makaranta na tsawon watanni bakwai a wannan shekara.”

‘Yan Najeriya da dama sun sha yin tsokaci game da wannan batu na ASUU, inda wasu ke cewa, ko da bashi ne ya kamata gwamnatin Buhari ta nemo shi domin dinke barakar zaman banza ta dalibai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here