Bincike: Jihohi 20 da Jam’iyyar APC na Iya Faɗuwa zaɓen 2023

 

Idan har ikirarin shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa rikicin cikin gida ne ya jawo musu faɗuwa a zaɓen Osun, kuma ya kasance Mai ɗorewa, APC na fuskantar faruwar irin haka a jihohi 20.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Mafi yawan rassan jam’iyyar APC na jihohi sun shiga cikin rikici sakamakon saɓani ko kuma wani abu da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani.

Binciken da aka gudanar a dukkan sassan ƙasar nan ya nuna cewa duk da kiran da shugaban ƙasa Buhari ya yi ga mambobin APC cewa kowa ya maida wuƙar shi kube, wasu da suka fusata basu ɗauki lamarin da sauki ba.

Yayin da wasu suka ɗauki matakin sauya jam’iyya, inda wasu suka koma PDP, wasu kuma suna nan daram a APC amma zasu iya komawa gefe su yaki jam’iyyar kamar yadda ta faru a jihar Osun.

Adamu ya ce rashin fahimtar juna a cikin gida da rashin haɗin kai ne ya jawo wa jam’iyyar APC rashin nasara a zaɓen jihar Osun.

Jerin Jihohin da haka ka iya faruwa da APC a 2023

Legit.ng Hausa ta haɗa muku jerin sunayen jihohin da APC ke fama da rikicin cikin gida, wanda idan abun da ya faru a Osun ya cigaba, jam’iyyar na fuskantar bazanar faɗuwa.

Jihohin sun haɗa da, Legas, Ondo, Eikiti, Ogun, Oyo, Abiya, Kano, Kaduna, Kebbi, Akwa Ibom, Ribas, Nasarawa, da jihar Benuwai.

Sauran jihohin su ne; Ebonyi, Kwara, Imo, Kuros Riba, Bauchi, Zamfara da kuma jihar Gombe.

Jam’iyyar APC na fuskantar yaƙi mai zafi yayin da babban zaɓen 2033 ke tafe. Bincike ya nuna matukar ba’a shawo kan mambobin da suka fusata ba, jam’iyyar ka iya faɗuwa a zaɓe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here