Tawaye: Zakuna Sun Kashe Shugabansu a Tanzaniya
Dandazon ma’aikata da masu ziyarar yawon buɗe ido a wani lambun shakatawa na cigaba da bayyana alhininsu bisa tsautsayin da ya fada wa wani shahararren zaki Bob Junior, wanda aka fi sani da suna Snyggve a shafukan intanet.
Zakin mai saukin hali, wanda hotunansa ke ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta, na da matukar kima a idon abokan hamayyarsa, ya kuma shugabancin namun dawan da ke dajin Serengeti na ƙasar Tanzaniya.
Inda ya shafe tsawon shekara bakwai yana zuba mulki a dajin tare da taimakon ɗan uwansa mai suna Tryggve.
Ana fargabar wasu ƙananan abokan hamayyarsa ne suka kashe shi.
Fredy Shirima, jami’i mai kula da gandun dajin na Serengeti, ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.
Ya ce “yawancin irin wannan al’amari yana faruwa ne a lokacin da shugaban dawa da ke mulki ya tsufa, ko kuma a wasu lokuta, idan mazajen zakuna ba sa farin ciki da yadda ake tafiyar da gandun dajin,” a cewar jami’in.
Read Also:
“Ana fargabar shima ɗan uwan nasa ya gamu da ajalinsa, sai dai muna ƙoƙarin tabbatar da hakan,” inji Mr Shirima.
Ya ƙara da cewa, an kashe ‘yan uwan biyu ne a lokuta daban-daban amma dai harin da aka kai musu shiryayye ne.
Wasu masana gandun daji sun bayyana cewa Bob Junior – wanda ake kyautata zaton ya kai shekaru 10 da haihuwa – ya ɗare kan karagar mulkin gandun dajin ne bayan rasuwar mahaifinsa mai suna Bob Marley, wanda ya shahara saboda kyawun halayyarsa a lokacin da yake raye.
Rahotanni sun bayyana cewa sarkin zakin Bob Junior, ya mutu ne a sanadiyyar harin da aka ƙaddamar masa kuma aka yi galaba a kansa sannan aka kasheshi a ranar Asabar.
Jami’an dake kula da gandun dabbobi suna shirye-shiryen gudanar da jana’iza ta musamman a wata rana ta daban da ba a bayyana ba.
Dajin Serengeti da ke arewacin ƙasar Tanzania, ya kasance gidan zama ga zakuna kusan 3,000, kuma ya shahara matuƙa ga masu yawon buɗe-ido na cikin gida da ƙasashen waje.
Masu tafiyar da aikin yawon buɗe-ido a ƙasar na cigaba da wallafa sakonnin jinjina a shafukan intanet bisa rasuwa sarkin dajin.