An Kai wa Dan Takarar Gwamnan Jihar Delta na jam’iyyar PDP Hari

 

Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Delta ya sha da kyar a hannun yan bindigar da ke farautar rayuwarsa bayan da suka budewa tawagarsa wuta.

Daya daga cikin jami’an tsaron dan takarar ya samu raunuka yayin da suke mayar da martani kan maharan kafin su gudu a cikin duhun dare.

Wannan ne karo na biyu da aka yi yunkurin hallaka dan takarar gwamnan PDP na Jihar Delta wanda shine shugaban majalisar wakilai ta Jihar, Rt Hon Sheriff Oborevwori.

Delta – Kasa da kwanaki hudu da ya rage a gudanar da zaben gwamnoni da yan majalisar jiha, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Hon Sheriff Oborerevwori, ya tsallake yunkurin kisan kai da aka shirya masa bayan da aka ruwaito yan bindiga sun mamayi tawagarsa a hanyar Warri/Sapele tare da bude musu wuta.

Oborerevwori, wanda shine kakakin majalisar jihar Delta, shi ne ya bayyana haka ranar Talata ta bakin sakataren yada labaransa, Mr Dennis Otu, The Nation ta rahoto.

Sanarwar ta ce shugaban majalisar yana dawowa daga Sapele zuwa Osubi lokacin da aka farmaki ayarin motocinsa. Sanarwar ta ce:

” Tawagar dan takarar gwamnan PDP na Jihar Delta, Rt Hon Sheriff Oborerevwori ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, 2023 sun gamu da mummunan hari daga yan bindigar da ba a san ko su waye ba tsakanin mararrabar Elume da Okuabude a karamar hukumar Okpe da ke Jihar.

”An farfasa motar da ya ke ciki da kuma motocin jami’an tsaron da ke ayarinsa da harsashi a harin da ya auku da misalin 9:05 na dare.

‘Ya ziyarci Sapele don tattauna batun siyasa kuma akan hanyarsa don komawa Osubi, yan bindigar da ba a san ko su waye ba suka tare tawagar tare da aiwatar da mummunan harin, suna sakin ruwan alburusai kan motarsa da sauran motocin ayarin. Banda kiyayewar Allah da kuma kasancewar motar da ya ke ciki bata jin harsashi ne ya ceci rayuwar dan takarar gwamnan mafi rinjayen a jihar.”

Ya cigaba da cewa:

”Jajirtattun jami’an tsaro da ke tawagarsa ne suka mayar da martani ga yan bindigar da ake kyautata zaton kwangilar kisan kai aka ba su inda suka shafe sama da mintuna 10 suna musayar wuta kafin daga bisani yan bindigar su gudu a cikin duhun dare. Duk da ba a rasa rai ba, daya daga cikin jami’an tsaron dan takarar yaji raunuka. An kai rahoton zuwa ofishin yan sanda don gudanar da bincike.

”Wannan ne karo na biyu da yan bindigar ke yunkurin daukar rayuwar dan takarar gwamnan na PDP a Jihar Delta, Rt Hon Sheriff Oborevwori.

”Na farkon ya faru ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, 2023, lokacin da ya tsallake yunkurin hallaka shi bayan da yan sanda suka bude wuta akan maharan a tawagarsa daga babban titin Warri/Sapele, lokacin da ke kan hanyar Koko, karamar hukumar Warri ta Arewa don bude katafariyar kasuwar zamani, ta Ogheye.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here