Daraktan ABSAA ya Shiga Hannu Kan Barazanar Kashe Masu Zabe

 

Tony Otuonye, daraktan hukumar tallace-tallace ta Jihar Abia ya shiga hannun jami’an DSS bisa barazanar kashe masu zabe.

Otuonye ya yi ikirarin kashe duk wani wanda ya ki zabar jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Abia ranar Asabar mai zuwa.

A cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya shaida cewa duk wanda zai kawo tsaiko ga nasarar Ahiwe na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, to zai kashe shi.

Abia – Hukumar tsaron farin kaya ta kama daraktan hukumar tallace tallace ta Jihar Abia, Tony Otuonye, bisa zargin barazanar kashe duk wanda ya ki zabar jam’iyyar PDP a Abia da dan takarar gwamnanta, Chief Okey Ahiwe, a zaben gwamnoni da za a gudanar Asabar mai zuwa.

Otuonye, a wani bidiyon yakin neman zabe da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya harzuka masu zabe da dama a Abia wanda suke da burin kada kuri’a, rahoton Punch.

An ruwaito cewa jami’an farin kaya sun kama shi, kuma ana ci gaba da neman abokan aikinsa.

A bidiyon, Otuonye ya ce zai kashe duk wanda zai kawo tsaiko ga nasarar Ahiwe na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Jihar.
Jam’iyyar PDP ta nesanta kanta da abin da Otuonye ya aikata

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta PDP ta nesanta kanta da Otuonye, tana mai cewa ba shi da izini daga jam’iyyar na tada rikici ko yi wa wani barazana.

Mukadashin sakataren watsa labarai na PDP, Abraham Amah, cikin wata sanarwa, ya musanta cewa jam’iyyar na shirin tada rikici yayin zabe, ya ce jam’iyyar ta masu son zaman lafiya ne.

Shugaban DSS na Abia ya ce an bada belin Otuonye

Direktan DSS ya fada wa wakilin Vanguard cewa an kama shugaban na ABSAA a ranar Litinin, an masa tambayoyi kan abin da ya aikata.

Ya ce:

“Eh, mun kama shi, mun masa tambayoyi kuma mun bashi beli. Yana asassa rikici.”

Da aka masa tambaya ko za a hukunta shi, shugaban na DSS ya ce ba a sallami wanda ake zargin ba.

“Belin ba ya nufin an wanke shi. Zai rika zuwa ofishin mu duk safe yayi zaben.”

Shugaban na DSS ya gargadi ya siyasa da magoya bayansu kan aikata duk wani abu da ka iya tada zaune tsaye a jihar.

Ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta sassautawa duk wani da aka samu yana neman jefa jihar cikin rikici ba.

naija news 247

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com