Jihohi 10 da ‘Yan Takarar Gwamnoni Sai Sun yi da Gaske a Zaben 2023

 

A hasashen da Legit.ng Hausa take yi, akwai wasu jihohin da sai an kai ruwa-rana a zaben Gwamnoni.

Daga cikin Jihohin nan akwai wadanda Gwamnoninsu ke neman tazarce a yankin Arewa maso gabas.

Sannan akwai inda Gwamnonin su na sa ran ‘Yan takaran jam’iyya mai-ci, su kai labari irinsu Kano.

Wannan rahoto ya tattaro maku Jihohin da za a kai gwauro, a kai mari a zaben makon nan.

1. Adamawa

Ahmadu Umaru Fintiri ba zai so ayi masa abin da ya yi wa Jibrila Bindow ba, idan ya yi sake Sanata Aisha Dahiru Binani za ta kafa tarihin zama Gwamna a kan sa.

Watakila Gwamnan na Adamawa ya hango tasirin mace a siyasar wannan karo, ya canza mataimakinsa da mace, a bana ya dauko Farfesa Kelatapawa Farauta.

2. Bauchi

Wani Gwamna da ke neman tazarce shi ne Bala Mohammad a jihar Bauchi. Tsohon Ministan zai fuskanci tsohon shugaban hafsun sojojin sama, Abubakar Siddique

Baya ga APC, Jam’iyyar NNPP ta tsaida Sanata Halliru Jika a matsayin ‘dan takaranta. Mafi yawan ‘yan siyasar Bauchi sun yi wa Gwamnan taron dangi a 2023.

3. Gombe

Zaben Gwamnan Gombe sai an tashi domin Inuwa Yahaya yana fuskantar kalubale musamman idan aka yi la’akari da sakamakon zaben shugaban kasa da majalisa.

Ana tunanin tsofaffin Gwamnoni biyu ba su goyon bayan tazarcen Inuwa, wannan ya karfafi PDP da Hon. Khamis Mailantarki mai neman mulki a jam’iyyar NNPP.

Jihohin da za ayi sabon zabe a 2023

4. Kano

Akwai yiwuwar takarar Nasiru Gawuna da Murtala Garo a APC sai an tashi a Kano domin ‘dan takaran NNPP, Abba Kabir Yusuf ya rabi farin jinin Rabiu Kwankwaso.

5. Kaduna

Sai Uba Sani da jam’iyyarsa sun yi da gaske a takarar Gwamna ganin yadda zaben baya ya kasance, bugu da kari da farin jinin Isa Ashiru Kudan a kauyukan Kaduna.

6. Katsina

Kamar dai Kano da Kaduna, akwai yiwuwar jam’iyyar PDP ta nemi kawo karshen shekaru takwas da APC tayi a Katsina, Lado Danmarke zai kara da Dikko Radda.

7. Kebbi

A hasashenmu, tsakanin Nasiru Idris na jam’iyyar APC da Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya da yake takara a PDP sai abin da aka gani a zaben Gwamnan jihar Kebbi.

8. Sokoto

Kamar yadda aka gwabza a 2019, babu mamaki kusan haka ya maimaita kan sa a zaben bana. Ahmad Aliyu zai tunkari ‘dan takaran PDP, Saidu Umar U/Doma a bana.

9. Oyo

Seyi Makinde yana cikin rukunin Gwamnonin da za su iya shan wahala kafin su zarce. ‘Dan takaran APC, Sanata Teslim Folarin zai iya doke PDP a jihar Oyo

10. Legas

Ba PDP ba, an fi ganin ‘dan takaran jam’iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour ne babban kalubalen da Babajide Sanwo Olu yake fuskanta a zaben Gwamnan Legas.

 

latest nigerian political news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com