Kamfanin Meta Zai Sake Korar Ma’aikata 10,000

Kamfanin Meta wanda shi ne ya mallaki shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya sanar cewa zai sake korar ma’aikata dubu goma.

Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin ke ɗaukar matakin korar ma’aikata da dama a baya-baya nan.

Wakiliyar BBC ta ce kamfanin Meta ya kori ma’aikata dubu goma sha ɗaya a cikin watanni huɗu da suka gabata, inda a yanzu ya sanar cewa zai sake sallamar dubban ma’aikatan sauran manyan kamfanoni fasaha irinsu Amazon da Microsoft suma sun kori dubban ma’aikata.

Kamfanoni fasaha sun samu matukar ci gaba a lokacin kullen annobar corona. Sai dai fargabar da aka nuna akan durkushewar tattalin arzikn duniya ta sa mutane sun rage amfani da kayayakin fasaha abinda ya sa kamfanonin suka dauki matakin korar ma’aikata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here