Zaman Lafiya ya fi Yaki – Tubabbun ‘Yan Boko Haram ga ‘Yan Najeriya
Rundunar sojojin Najeriya a jahar Borno ta tabbatar da karbar wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da suka tuba.
‘Yan ta’addan sun mika wuya ne tare da bayyana nadamar ayyukansu da suka aikata na ta’addanci.
Hakazalika sun roki ‘yan Najeriya da su taimaka su yafe musu, kuma sun yi alkawarin wanzar da zaman laifiya.
Maiduguri, Borno – Rahoto daga Daily Trust na shaida cewa, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.
A cewar majiyoyin sojoji, ‘yan ta’adda 190 sun mika wuya a karamar hukumar Mafa da ke jahar Borno a ranar Asabar.
Read Also:
An tattaro cewa mazauna garin sun yi mamaki lokacin da suka ga dimbin ‘yan ta’addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar.
A cewar majiyar tsaro, wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayaka, sojojin kafa, matansu da yaransu.
‘Yan ta’addan da suka mika wuya sun kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su gafarta musu tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa sun mika wuya cikin son rai, suna masu cewa zaman lafiya ya fi yaki.
Wannan ne karo na farko da ‘yan Boko Haram suka mika wuya ga sojoji?
Idan mai karatu zai tuna, sojojin Najeriya sun yi ikirarin cewa jimillar ‘yan ta’addan Boko Haram 1081 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin a cikin makonni biyu da suka gabata.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan masu tayar da kayar baya da suka mika wuya sun roki ‘yan Najeriya da su yafe masu.
Rokon nasu ya haifar da martani iri-iri kamar yadda wasu mutane suka ce ba su cancanci jinkai ba dangane da abubuwan da suka gabata.