Jahar Zamfara na Fama da ‘Yan Cirani a Jahar da Sukai 784,000 – Hajiya Fa’ika
Kwamishinar da ke lura da ayyukan jinkai da agajin gaggawa ta jahar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Hajiya Fa’ika Ahmad, ta ce suna ta fama da ‘yan cirani a jahar da sukai 784,000.
Ta ce cikin adadin akwai sama da 184,000 da suke mata sai kuma kananan yara da suka kai 600,000.
Read Also:
Fa’ika ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da take karbar kayan abinci da kuma wasu sauran kayan jinkai da ma’aikatar agaji ta kasa ta bayar.
Mataimaki na musamman ga Minista Sadiya Faruk, Alhaji Musa Ahmad Bungudu ne ya mika kayan ga hukumomin jahar.
Kwamishinar ta ce akwai tashin hankali idan aka kalli adadin mata da yaran da suka samu kansu cikin wannan yanayi, dan haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa.
Wannan dai na zuwa ne lokacin da Najeriya ta karbi ‘yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.