Rashin Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta Bada Umarnin Rufe Kasuwannin Jahar

 

Matsalar tsaro a jahar Zamfara ta yi tsamari kuma gwamnatin jahar na shirin daukar matakan kare al’ummarta.

Wasu gungun ‘yan bindiga a jahar Zamfara sun mamaye garuruwa da dama inda suke sace mutane don neman kudin fansa.

Makarantu da sauran cibiyoyin ilimi suma sun fuskanci hare-hare daga miyagun waɗanda ba su nuna jin ƙai a yayin aikinsu.

Zamfara – An rufe dukkan manyan kasuwannin jahar Zamfara sakamakon umarnin Gwamna Bello Matawalle.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya rawaito, gwamnan ya kuma bayar da umurnin rufe dukkan gidajen mai dake yankunan.

Ya kuma ba da umarnin cewa kada a sayar da mai ko da a cikin jarkoki.

TVC News ta rahoto cewa Matawalle ya ce matakin ya zama dole idan aka yi la’akari da dawowar fashi da makami da garkuwa da mutane a jahar.

Ya kuma umarci jami’an tsaro da su harbi kowane babur da ke dauke da mutane sama da biyu idan suka ki tsayawa don a kama su.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here