Majalisar Dokokin Jahar Plateau ta Nemi Mazauna Jahar da su Kare Kansu da Hare-Hare

 

An bukaci mazauna jahar Filato da su kare kansu daga hare-hare yayin da rikici ke ci gaba da kamari.

Majalisar dokokin jahar Filato ce ta yi kiran inda ta yi ikirarin cewa tsaro na yau da kullun ba zai iya taimaka wa jama’a ba.

A halin yanzu, ‘yan majalisar sun aike da kudiri ga gwamna Lalong kan yadda za a maido da zaman lafiya a jahar.

Filato – Majalisar dokokin jahar Filato ta nemi mazauna yankin da su kare kansu. Jahar ta fada cikin rikici a ‘yan makonni biyu da suka gabata.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Jos, babban birnin jahar Filato, a ranar Juma’a, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Dasun Philip Peter, ya ce tsarin tsaro na yau da kullun ba zai iya ba da tabbacin tsaro ba.

Ya kuma ba Gwamna Simon Lalong makonni biyu ya yi aiki da kudurorin da ta gabatar masa kan yadda za a maido da zaman lafiya.

Peter ya ce ‘yan majalisar za su dauki mataki idan gwamnati ta kasa daukar mataki cikin wa’adin makonni biyu.

Ya bukaci jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan ta’asar tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce:

“A madadin Majalisar Dokokin Jahar Filato, ina so in jajantawa Gwamnati da Jama’ar Jahar Filato kan kashe -kashen dabbanci da kisan gilla da ke faruwa a cikin garuruwan Bassa, Barkin Ladi, Bokkos, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu , Mangu, Riyom, Jami’ar Jos da kuma na kwanan nan a Yelwa Zangam.

“Majalisar ta yi Allah wadai da dukkan wadannan kashe-kashen baki daya, duk wadannan kashe-kashen ba abin karba ba ne kuma abin Allah wadai ne. Muna jajantawa iyalan duk waɗanda suka rasa masoyansu a lokacin waɗannan hare-haren.

“Muna kira da babbar murya ga mutanen Filato da su tashi tsaye don kare kansu da garuruwansu, saboda tsarin tsaro na yau da kullun baya ba da tabbacin tsaron lafiyar mu a matsayin mu na mutane.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here